Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Taron PDP na Tabbatar da Shugaba Jonathan


PDP

A yau dai ake babban taro na Jam’iyyar PDP, inda za’a tabbatarwa shugaba Jonathan tikitin tsayawa takara domin zaben watan Fabarairu na shekara mai zuwa.

Wakilin Muryar Amurka Nasiru Adamu El-Hikaya ya halarci wannan babban taron a dandalin eagle square Abuja, inda ya zanta da mataimakin sakataren yada labarai na jam’iyyar PDP na kasa.

Da yake Magana da wakilin mu mataimakin sakataren yada labaran Barista Abdullahi Jalo yace, suna sa ran cewa mutane ne masu tarin yawa zasu halarci wannan taron wanda jamiyyar zata tabbatarwa shugaba Jonathan da tikitin tsayawa takaran shugabancin Najeriya a zabe mai zuwa

Barista Jalo yace suna sa rai cewa a kalla kowace jiha mutane kusan dubu biyar ne zasu zo daga ko wace jiha, wanda dubu biyar sau 36 sune adadin jamaar da ake has ashen su halarci taron.

Yace jimlar jamaar zasu kai dubu 180 abinda yace dandalin na Eagle Square ba zai iya dauka ba.

To sai dai da wakilin namu ya tambaye shi tunda Shugaba Jonathan bai da abokin gogawa akwai wani bukatar zabe ne? ko dai za a shafa ne a waste?

Amma Barista yace ko kusa ‘’Kasan dokar jamiyyar PDP baya kama karya, ko kai kadai ne sai an jefa maka kuria’’

Wannan babban taro na PDP bazai rasa kalubale ba saboda wata shari’a da Dakta Ardo ya shigar a babbar kotun tarayya, da za’a fara shari’ar wajen tsakiyar watan nan da ake bukatar dakatar da shugaba Jonathan daga takarar, domin cewa wannan tamkar tazarce ne karo na uku.

please wait

No media source currently available

0:00 0:01:49 0:00
Shiga Kai Tsaye

XS
SM
MD
LG