Kwamitin gaggawa na hukumar ta WHO yayi wani taro a jiya talata domin duba hadarin dake tattare da bazuwar wannan cutar a kasar da za a gudanar dawannan taron musammam ma a birane irin su Rio de Janeiro.
Yan kwamitin suka ce kamuwa da wannan cutar ga kowanne mutum duk iri daya yake ko a wajen taro ko kuma mutum yana shi kadai, suka ce kuma ana iya yin riga gafi tun kafin kamuwa da cutar.
Hukumar tace hadarin dake tattare da bazuwar wannan cutar dai ba wani mai barazana bane sai dai kuma da yake za a gudanar da gasar na Olympic a cikin watan Agusta ne kana za a kuma yi na nakasassu a cikin watan satunba, wanda kila hakan zai iya baza cutar.
Za a dai gudanar da gasar ne a cikin lokacin sanyi a kasar ta Brazil , wanda kuma barazanar bazuwar cutar kalilan ce.
Haka kuma hukumar ta W H O tace mahukuntar kasar Brazil din na nan na iya bakin kokarin su domin magance yawaitan sauro a kasar.