Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Tarzoma Ta Barke A Kasar Zambiya


Shugaban hamayya na kasar Zambiya, Michael "King Cobra" Sata (a tsakiya), yana barin rumfar zabe bayan jefa kuri'arsa ranar talata 20 Satumba 2011a Lusaka.

'Yan hamayya a tsakiyar arewacin kasar su na nuna fusata da tafiyar hawainiya wajen kidaya kuri'u da bayyana sakamakon zaben shugaban kasa da aka yi ranar talata

Tarzoma ta barke a yankin tsakiyar arewacin kasar Zambiya, inda magoya bayan jam’iyyun hamayya ke nuna fusata da jan kafar da ake yi wajen kidaya kuri’un da aka kada a zaben shugaban kasa na ranar talata.

‘Yan sanda sun ce masu zanga-zanga sun jefi motoci da gine-gine yau alhamis a biranen Kitwe da Ndola, sun kuma cinna wuta a wata kasuwa a Kitwe. Shugaban ‘yan sandan yankin, Martin Malama, ya fadawa ‘yan jarida cewa ‘yan sanda su na kokarin kwantar da wutar wannan fitina.

Sakamako na baya-bayan nan da hukumar zabe ta Zambiya ta bayar, a bayan da aka kidaya kimanin rabin mazabun kasar, ya nuna shugaban hamayya Michael Sata yana gaba da kashi 43 cikin 100, yayin da shugaba mai-ci, Rupiah Banda, yake biye da kashi 36 cikin 100.

Amma kidayar kuri’un tana tafiyar hawainiya fiye da yadda aka zata, kuma ‘yan kallo sun yi hasashen cewa hukumar zaben ba zata iya bayyana cikakken sakamako a cikin wa’adin da ta dibar ma kanta na yau alhamis ba.

Tankiya ta karu jiya laraba a lokacin da babbar kotun kasar Zambiya ta haramta ma wasu kafofin labarai guda uku masu zaman kansu buga rahotannin rade-radi game da sakamakon zaben. Wannan umurni na kotun ya zo ne a bayan da jaridar “The Post” ta buga wani labari mai taken “Sata ya doshi samun nasara.”

Daga bisani, ofishin shugaban kasar ya bayar da sanarwa yana yin watsi da rade-radin cewa an kammala hada sakamakon zaben, kuma har an sanar da shugaba Ban

XS
SM
MD
LG