Accessibility links

Tashin wani bam a kasar Syria ya raunana sojoji shidda

  • Jummai Ali

Barnar da tashin bam ya yiwa wata motar soja a Daraa

Wani bam daya tashi a gefen hanya a Syria kusa da kwambar tawagar jami’an sa ido na Majalisar Dinkin Duniya a yau Laraba ya raunana sojojin Syria guda shidda.

Wani bam daya tashi a gefen hanya a Syria kusa da kwambar tawagar jami’an Majalisar Dinkin Duniya na nazari a yau Laraba ya raunana sojojin Syria guda shidda. Wannan al’amari ya faru ne, kwana daya bayan da mai shiga tsakani na kasa da kasa Kofi Anan ya yi kashedin cewa ci gaba da boren da ake wa gwamnati zai iya kaiwa ga barkewar yakin basasa a kasar.

Tashin bam din na gefen hanya ya auku a birnin Daraa mai fama da tashin hankali da ke kudancin kasar. Jagoran tawagar jami’an Majalisar Dinkin Duniya, Janaral Robert Mood, na cikin tawagar to amman da shi Mood din da sauran jami’ai masu nazarin al'amurra a kasar, babu wanda ya sami rauni.

Jami’an sa idon suna ta safa da marwa a duk fadin Syria domin ganin ko ana kiyaye yarjejeniyar tsagaita bude wutar wadda ke kasa tana dabo. Yarjejeniyar bangare ne na shirin samun zaman lafiyar da Mr Annan ya shiga tsakani aka shata.

A jiya Talata, Mr. Annan ya ce aikin sa idon, da alamar shi ne kadai damar da ta rage ta samar da zaman lafiya a Syria. Bayan wani taron manema labaran da kwamitin sulhu na Majalisar Dinkin Duniya ya kira, Mr. Annan ya gaya wa manema labarai cewa akawai matukar barazanar cewa idan ba a yi hakan ba to fa kasar na iya fadawa cikin yakin basasa.

A halin da ake ciki kuma, gwamnatin Syria ta cigaba da kidaya kuri’un zaben ‘yan Majalisar da aka gudanar ranar Litinin, wanda ‘yan adawa su ka yi watsi da shi a zaman shirme.

XS
SM
MD
LG