Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Tashar Wutar Lantarki da Za’a Gina a Tsaunin Mambila Zata Samar da Wuta Mega Watts 3000


Shugabannin garuruwan dake tsaunin Mambila
Shugabannin garuruwan dake tsaunin Mambila

Baicin kokarin inganta ayyukan noma da tsaro da gwamnatin Buhari ta yi, yanzu ta koma ga batu samun wutar lantarki a tsaunin Mambila dake jihar Taraba inda tuni ta rattaba hannu akan kwangila da wani bankin kasar China.

Tashar da za’a gina a tsaunin Mambila zata samar da wuta mega watts dubu uku.

A wata kasuwa akan tsaunin Mambila din, a garin Ngoroje jama’a dake hada hadar kasuwanci na fatan tashar zata tabbata saboda wasunsu na cewa tun suna yara suke jin za’a gina tashar. Wai tun a shekarar 1960 suke jin labarin gina tashar.

Ministan ma’aikatar ayyuka, gidaje da makamashi Barrister Babatunde Fashola shi ya sanar da ba da kwangilar kan kudi dalar Amurka biliyan biyar da miliyan dari bakwai da casa’in da biyu, $5’792b. Cikin kudin, kashi goma sha biyar ne kacal gwamnatin Najeriya zata biya, sauran kuma na ‘yan kwangilan ne da suka fito daga China.

Wazirin Mambila Sanata Marafa Bashir Abba ya nuna farin ciki da sabon matakin. Yace akwai alamu za’a yi aikin yanzu saboda ‘yan China sun fara isa wurin suna zagayawa tare da jibge wasu kayan aiki. Shi ma sakataren magoya bayan Buhari na da kwarin gwuiwar aikin zai kai ga gaci.

Injiniya Ahmed Guroje na kungiyar wanzar da zaman lafiya ya bukaci al’ummar yankin su zauna lafiya domin karfafa wa masu kwangilar gwuiwa tare da cin gajiyar aikin.

Ga rahoton Nasir Adamu El-Hikaya da karin bayani

please wait

No media source currently available

0:00 0:02:54 0:00

Facebook Forum

Hawan Nasarawa, jihar Kano a Najeriya, lokacin da aka gudanar da bukukuwan Sallar Eid el Fitr
please wait

No media source currently available

0:00 0:03:44 0:00
Karin bayani akan Rahotannin Taskar VOA
XS
SM
MD
LG