Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Tashin Hankali: An Kafa Dokar Hana Fita A Bwari Daga Karfe 6 Na Yamma Zuwa 6 Na Asuba


Ministan Yankin Tarayya, Abuja Muhammad Musa Bello
Ministan Yankin Tarayya, Abuja Muhammad Musa Bello

Yayin da ake harmar bukin Kirsimeti, a wani bangare wata rigima ta barke tsakanin wasu majiya karfi a Karamar Hukumar Bwari da ke yankin Birnin Tarayyar Najeriya, Abuja, wanda ya yi sanadin mace-mace da asarar dukiyoyi na miliyoyin naira. Hukumomi dai sun ce sun kwantar da kurar.

Sakamakon wani tashin hankalin da ya yi sanadin mutuwar wasu mutane uku baya ga dukiyoyin miliyoyin nairori da aka salwantar sanadiyyar kone-konen da ya biyo baya a Karamar Hukumar Bwari, Ministan Birnin Tarayyar Najeriya, Abuja, Muhammad Musa Bello, ya sanar da kafa dokar hana fita a fadin Karamar Hukumar daga karfe shida na yamma zuwa karfe shida na asuba agogon Najeriya.

Bayan da Ministan na Birnin Tarayyar Najeriya ya yi shelar kafa dokar hana fita din, sai mai magana da yawun Ministan, Abubakar Sani, ya gaya ma Hassan Maina Kaina, wakilin Sashin Hausa Na Muryar Amurka cewa fada ne ya gaure tsakanin wasu matasa, wanda ya kai ga daba ma dayan wuka. Ya ce daga nan ne fa gari ya yamutse har tashin hankalin da ya biyo baya ya kai ga kone-konen kaddarori ciki har da babbar kasuwar Bwari.

Kakakin Rundunar ‘yan sandan Binrin Tarayya, Abuja ASP Anjuguri Manzah ya tabbatar da aukuwar lamarin. Amma ya ce an shawo kan lamarin. Manzah ya ce za a kaddamar da bincike saboda a gano musabbabin tashin hankalin a kuma hukunta duk mai laifi.

Ga dai wakilinmu Hassan Maina Kaina da cikakken rahoton:

please wait

No media source currently available

0:00 0:02:49 0:00

Facebook Forum

XS
SM
MD
LG