Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Tashin Kudin Dala Ya Jefa Wasu Yan Kasuwa Cikin Wani Hali A Najeriya


Wani dan canji yan kirga kudi.
Wani dan canji yan kirga kudi.

Sakamakon matsalar tashin dala a Najeriya, yanzu haka yan kasuwa da ke sayo motoci daga kasashen waje, na cewa yanayin da ake ciki ya tilasta musu dakatar da fita waje domin sayo motocin, saboda karyewa da kudin Nigeriya wato Naira ta yi idan aka kwatanta da dalar Amurka.

To sai dai kuma a wani bangaren, yanzu yan kasuwa na cin karensu babu babbaka sakamakon wannan matsala, inda komi yayi tashin gwauron zabi a kasuwanni.

Matsalar tashin Dalar tayi tsanani a jihar Adamawa da Taraba, inda ta kai akan canza Dala kusan Naira 400 a kudin Najeriya, lamarin da kan shafi harkokin kasuwanci a yanzu kama daga kayayyakin masarufi zuwa kayan more rayuwa.

A cewar wasu mazauna wadannan jihohi sun koka ne kan yadda farashin kayayyaki ke tashi, sai kuma ace Dala ta tashi, ko kayayyakin da ake sarrafawa a cikin gida na tashi wanda basu da wata alaka da Dala.

Tashin Dalar dai ya shafi yan Kasuwa dake shigowa da kayayyaki da ma motoci daga kasashen waje, haka kuma suma mutanen da ke sayan kayan.

Domin karin bayani.

please wait

No media source currently available

0:00 0:03:49 0:00

Hawan Nasarawa, jihar Kano a Najeriya, lokacin da aka gudanar da bukukuwan Sallar Eid el Fitr
please wait

No media source currently available

0:00 0:03:44 0:00
Karin bayani akan Rahotannin Taskar VOA
XS
SM
MD
LG