Karatowar babban zaben Najeriya, a tsakirar watan gobe, na kara jan hankalin masu zaben, wajen nazarin yadda zaben zai gudana ba tare da musgunawa, dage zaben koma sauya alkaluma ba.
Shin hukumar zaben nada dukkan kudade, kayan aiki koko ma’aikatan da zasu gudanar da zaben, idan aka kauda raba katunan zabe, na dindindin, da wasu har yanzu basu samu ba, da sauyawa Kwamisinonin zabe na jihohin wajen aiki, ba wani cikkaken bayanin buga takardun zaben da yawan wadanda suka samu rajista zuwa yanzu.
Mataimakin Darektan hulda da jam’a, na hukumar zaben, Nic Dazan, yace wadanda aka yiwa rajista, a zaben daya gabata na 2011, ‘yan shekaru goma sha takwas, zuwa sama addadin su ya kai miliyan saba’in da biyu, kuma an basu kati na wucin gadi kana daga bisani sun karbi na dindindin.
Wasu daga cikin masu zabe sun bayana tasirin a kasa a tsare wato a tsayawa don jin sakamakon zaben a runfunan zaben, kan gudanar da zabe cikin kwanciyar hankalin da adalci.