Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Tasirin Gwamnatoci a Kowane Mataki


Najeriya

Karfi da Hakkokin Gwamnatoci a Kowane Mataki.

Idan a na maganar gwamnati, to lallaine akawo batun a kowane mataki, sanin kowane cewar a tsari irin na kasar Najeriya ana da matakai uku na gwamnatoci, wato gwamnatin tarayya, gwamnatin jiha, da gwamnatin karamar hukuma.

Wadannan gwamnatocin a kowane mataki na da irin nasu ayukan da sukeyi ma al’umah, kuma kowane daga cikin su na da nasu tsarin gudanaewar. Idan muka dauki gwamnatin tarayya za’a ga cewar itace wada take da hakin rike dukiyar kasa baki daya, kuma tana da wasu ayyuka da takanyi don cigaban kasa, misalli za’a ga cewar hakin gwamnatin tarayyane ta yi tituna da zasu hada waccan jihar zuwa wata, kokuwa ita zata samar da hanyar da za’abi wajen kasafin kudin kasa.

Ta daya hannun kuma za’a ga cewar gwamnatin jiha ita keda hakin yin aiki mafi yawa ga jama’a, wanda tafi gwamnatin tarayya kusanci da talakawa, kuma ita tafi yima al’umah aiki a kan gwamnatin tarayya. Sai gwamnatin kanana hukumomi, wadanda suma aikin su ne su samar da wasu abubuwan more rayuwa ga ‘yan kasa.

Duk dai yadda akace gwanatin jiha suna da matukar mahimanci ga al’uma kuma da cigaban kasa. Don haka kada al’uma suyi wasa da zaben wadanda zasu jagorance su a jihohinsu.

Tasirin Gwamnatoci - 4'11"
please wait

No media source currently available

0:00 0:04:05 0:00
Shiga Kai Tsaye

  • 16x9 Image

    Yusuf Harande

    Yusuf Aliyu Harande, dan jarida da ke aiki da Sashen Hausa na Muryar Amurka (VOA). Yana da kwarewa a fannoni da dama, da suka hada da shafukan yanar gizo, talabijin, bincike, rubutu da hotuna. Dan asalin kauyen Hiliya ne daga karamar Hukumar Tambuwar a jihar Sakkwato.

Shin PI Za Ta Fashe Kuwa Ko Yaudara Ce Kawai?

Karin bayani akan Bidiyo
XS
SM
MD
LG