Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Tawagar Majalisar Dattawan Amurka Ta Dawo Daga Zawarcin Afrika


Shugaban kungiyar AU Moussa Faki Mahamat
Shugaban kungiyar AU Moussa Faki Mahamat

A wata hobbasa ta kyautata dangantakar Amurka da Afurka, 'yan jam'iyyar biyu mafiya tasiri a Amurka wato Republican da Democrats, sun je Afurka, inda su ka tattauna da shugabanni tare da bayyana manufar Amurka.

Wata tawaga ta Sanatocin Amurka 5 daga jam’iyyu biyu, ta dawo daga ziyarar tsawon mako guda a kasashen Afirka hudu, inda ta je don jaddada kudurin Amurka na taimaka ma nahiyar.

“Mu dinnan 5 mun je ne da zummar jaddada muhimmancin huldar Amurka da Afirka, kuma an mana kyakkyawar tarba. Kuma ina ganin mun cimma burinmu, “ abin da Sanata Chris Coons, dan jam’iyyar Democrat ya gaya ma manema labarai kenan.

To amma Sanata Coons ya kuma yi nuni da cewa sun amsa tambayoyi game da Shugaban Amurka Donald Trump, da kuma alamar rashin son dasawa da Afirka, saboda gibin da ke akwai a diflomasiyyance da kuma kalaman cin mutunci da Trump ya yi.

Facebook Forum

XS
SM
MD
LG