Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Tawagar Majilisar Dinkin Duniya Ta Tafi Myanmar


Aung San Suu Kyi (d) conversa con el general Zaw Win (i), viceministro de Asuntos Fronterizos, durante el desfile por el Día de las Fuerzas Armadas en Birmania.

Yanzu haka dai majilisar dinkin duniya ta aike da tawagar ta zuwa kassar Myanmar domin duba halin da 'yan jisin Rohingya suke ciki tare da basukayan tallafi

A yau Alhamis ne MDD ke shirin aikawa da wata kakkarfar tawagar wakilanta zuwa jihar Rakhine ta kasar Myanmar don su je suga wainar da ake toyawa a yankin, a daidai lokacinda majalisar ke kokarin ganin an dada tura kayan agaji ga ‘yan jinsin Rohingya dake can.

Kakakin MDD din, Stephane Dujarric, wanda ya bada wannan bayanin, yace fatar Majalisar itace cewa wannan matakin na farko da Majalisar ta dauka ya bude hanyar da za’a kara habakarda aiyukkan kai kayan tallafawa wadanan mutanen dake jin jiki matuka.

Wannan tafiyar da tawaggar wakilan MDD din zasu soma a yau Alhamis zuwa jihar ta Rakhine, itace karo na farko da aka yi irinta tun daga lokacinda ‘yan Rohingya din suka soma gudun hijiran barin kasar tasu.

MDD na kiyasin cewa Musulmin Rohingya su fiyeda 400,000 ne suka gudu daga Myanmar zuwa kasar Bangladesh don gujewa azabar da hukumomin Myanmar ke nuna musu.

A cikin kwannaki biyu kacal da suka gabata, mutane 45,000 suka tsere daga Myanmar zuwa can Bangladesh.

Facebook Forum

Laftanar Janar Farouk Yahaya

Makasan Sheikh Goni Aisami Sun Bata Sunan Sojin Najeriya – Laftanar Janar Farouk Yahaya
please wait

No media source currently available

0:00 0:02:11 0:00
Karin bayani akan Bidiyo

Shin da gaske NNPP ba ta yi wa Shekarau adalci ba?

Karin bayani akan Bidiyo
XS
SM
MD
LG