Wata tawagar kungiyar Taliban ta kai ziyara Moscow, babban birnin Rasha, inda ta gana da jami’an kasar, mako guda bayan da Amurka ta soke wata tattaunawa da kungiyar ta Taliban kan zaman dakarun Amurka a kasar ta Afghanistan.
Kafafen yada labaran Rasha, sun ruwaito Kakakin kungiyar ta Taliban, Suhail Shaheen, yana cewa tawagarsu ta hadu da wakilin shugaban Rasha kan rikicin na Afghanistan Zamir Kabulov a jiya Juma’a, sun kuma tattauna kan matakan da ake bi don maido da zaman lafiya a Afghanistan.
A wani labari kuma, a jiya Juma’a shugaban kasar ta Afghnistan Ashraf Gani, ya fadawa wani gangamin yakin neman zabe cewa, an kashe sama da mayakan kungiyar ta Taliban dubu biyu cikin makon da ya gabata.
Ya kara da cewa gwamnatinsa ce kadai mafita ga ‘ya’yan kungiyar idan suna neman sulhu.