Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Tilas Rasha Ta Kawo Karshen Rikicin Gabashin Ukraine In Ji Amurka


Kawo karshen rikicin gabashin Ukraine ya ta' allaka ne akan kasar Rasha kuma ya zama wajibi da dauki matakan kawso karshen sa.

A ziyararsa ta farko a Kyiv a yau dinnan Lahadi, Sakataren Harkokin Wajen Amurka, Rex Tillerson, ya ce Amurka ta gaya ma Rasha cewa dole ne fa ta dau mataki na farko na kawo karshen tashin hankali a Gabashin Ukraine.

Tillerson ya yi jawabin ne ganga da Shugaban Ukraine Petro Poroshenko bayan da mutane biyun su ka gana don tattauna yadda za a kawo karshen tashin hankali a Gabashin Ukraine ta kuma goyi bayan kokarin Ukraine na sauye-sauye.

"Ina da kwarin gwiwar cewa muddun wadanda abin ya shafa su ka dukufa ga cimma wannan burin, za mu samu cigaba," a cewar Tillerson, yayin da ya ke nuni da yarjajjeniyar da aka cimma a Minsk - wadda yarjajjeniya ce ta kwance damara da Rasha da Ukraine su ka cimma a 2015.

Tillerson ya nada tsohon Jakadan Amurka a kungiyar Kawance ta NATO Kurt Volker a matsayin wakili a tattaunawa kan Ukraine.

Facebook Forum

XS
SM
MD
LG