Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Trump Da Tsoffin Jami'an CIA sun Sa Kafar Wando Guda


Shugaba Donald Trump
Shugaba Donald Trump

Takun sakar da ake yi tsakanin Shugaban Amurka Donald Trump da wasu tsoffin jami'an CIA ya dau wani sabon salo ta yadda Shugaba Trump ya dau matakin soke takardar tabbatar da zama masanin tsaro ta wasu daga cikinsu.

Zaman doya da manja tsakanin Fadar Shugaban Amurka da bangaren jami’an tsaron farin kaya na karuwa, yayin da Shugaba Donald Trump da tsohon babban shugaban jami’an tsaron farin kaya ke ta kace-nace kan takardar tabbatar zama masanin tsaro.

Jiya Jumma’a Shugaba Trump ya kai bugunsa na farko a wannan dauki ba dadin da ake yi, ya na mai barazanar janye takardar tabbatar zama masanin tsaro ta wani babban jami’in Ma’aikatar Shari’a, sannan ya kare shawarar da ya yanke ta soke takardar tabbatar da zama masanin tsaro ta tsohon shugaban hukumar leken asirin tsaron kasa ta CIA John Brennan tare da cewa mutane da dama sun yaba da hakan.

Daga bisani, tsofin jami’an hukumar CIA sun mai da martani, inda fiye da 60 daga cikinsu su ka rattaba hannu kan wata takarda ta yi Allah wadai da abin da su ka kira, “ramuwar gayyar siyasa kan jami’an tsaron farin kaya da sauran kwararru kan harkar tsaro.”

Facebook Forum

Hawan Nasarawa, jihar Kano a Najeriya, lokacin da aka gudanar da bukukuwan Sallar Eid el Fitr
please wait

No media source currently available

0:00 0:03:44 0:00
Karin bayani akan Rahotannin Taskar VOA
XS
SM
MD
LG