Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Trump Dan Takarar Shugabancin Amurka Na Republican Ya Caccaki Hillary Clinton


Donald Trump na jam'iyyar Republican

Yayinda aski ya soma kawo gaba goshi Donald Trump na jam'iyyar Republican dake kyautata zaton zai fafata da Hillary Clinton ta Democrats ya caccaketa da nufin batata gaban masu kada kuir'a

Dan takarar shugabancin Amurka a karkashin jam'iyyar Republican Donald Trump, jiya Laraba, ya caccaki Hillary Clinton, yace abokiyar takararsa ta jam'iyyar Democrat, "tana iya zama mutuniyar da ta dara ko wani dan takara da ya taba neman shugabancin Amurka rashin gaskiya, ita kuma Clinton ta maida martani cewa, zarge zargen nasa ba wani abu bane illa karairayi."

A cikin jawabin da yayi jiya a birnin New York yayinda nagoya bayansa suke sowa, Trump ya zargi tsohuwar sakatariyar harkokin wajen na Amurka cewa, ta goyi bayan manufofin Amurka a kasashen waje wadanda suka haifarda "kashe kashe da lalata dukiya, da janyo ta'addanci" yayinda take rike da wannan mukamin tsakanin shekara ta 2009-2013, sannan daga bisani ta arzurta kanta da miliyoyin dala ta wajen gabatar da jawabai da ake biynata da wadannan kudade.

Sukar da Trump ya yiwa Clinton, ta zo ne kwana daya bayanda tayi kaca-kaca da ikirarin cewa shi mutum ne daya kware ta fuskar kasuwanci, ta ambaci matakan da ya dauka har sau hudu na ayyana kamfaninsa a zaman wanda hanun jarinsa ya karye.

Nijar, Fulani, Wodaabe

Yadda Funalin Wodaabe Suka Gudanar Da Gasar Nuna Kyau A Nijar
please wait

No media source currently available

0:00 0:02:22 0:00
Karin bayani akan Rahotannin Taskar VOA

Sauyin yanayi : Yankin Sahel na Afrika

Yadda Sauyin Yanayi Ke Rura Wutar Rikici A Yankin Sahel
please wait

No media source currently available

0:00 0:12:44 0:00
Karin bayani akan Rahotannin Taskar VOA
XS
SM
MD
LG