Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Trump Ya Baiwa Yan Majalisa Kwanaki 60 Su Dauki Mataki Akan Shirin DACA


Wasu daga cikin masu goyon bayan shirin DACA ke tattakin nuna rashin goyon bayan ruguje shirin jim Kadan bayan sanarwar yiwuwar ruguje shi.

Ana cigaba da cece kuce akan yiwuwar ruguje shirin kariya ga Yara 'ya'yan bakin haure masara izinin zama a Amurka wanda akewa lakabi da DACA a takaice.

Shugaba Donald Trump yace zai waiwayi shawarar daya yanke ta kawo karshen shirin kare Yara yayan bakin haure marasa izinin zama kusan dubu 800,000 kaucewa maida su kasashen su idan yan majalisa basu yi wani abu akan lamarin ba.

Sa’o’i bayan Jami’an gwamnati sun ce baza a kara karbar takardar shiga cikin shirin na DACA ba, Trump ya rubuta a twitter a yammacin Talata cewa “Yan majalisa na da watanni shida su halatta DACA (Wani abu da gwamnatin Obama ta kasa yi). Idan sun kasa yace zai sake waiwayar lamarin!”

Masu zanga zangar nuna rashin amincewa wannan mataki sun taru a biranen Washington da Los Angeles da New York da kuma Denver da sauran birane.

Wani d'an raji mai suna Gustavo Torres ya shaidawa taron jama’a a gaban White House cewa: “Wannan shugaban kasar yayi wa al’ummar mu karya… Ya fada mana yana kaunar mu masu burin wato Dreamers.’ Amma yayi mana karya a saboda haka shi Makaryacine!”

Facebook Forum

Laftanar Janar Farouk Yahaya

Makasan Sheikh Goni Aisami Sun Bata Sunan Sojin Najeriya – Laftanar Janar Farouk Yahaya
please wait

No media source currently available

0:00 0:02:11 0:00
Karin bayani akan Bidiyo

Shin da gaske NNPP ba ta yi wa Shekarau adalci ba?

Karin bayani akan Bidiyo
XS
SM
MD
LG