Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Trump Ya Ce Baya Neman Yaki Da Kasar Iran


Shugaban Amurka Donald Trump ya ce baya neman yaki da kasar Iran kuma yana niyar tattaunawa da shugabanninta ba tare da wasu sharuda ba, amma kuma ya ce ba za a kyaleta ta ci gaba kera makaman kare dangi na nukiliya ba.

Trump ya fadawa taron manema labaran NBC cewa idan Amurka ta shiga yaki da Iran za a ga abin da ba a taba gani ba, saboda lamarin zai yi muni matuka.

Amma kuma ya kara da cewa shi ba haka yake bukatar ba.

Shugaban na Amurka ya ce ba zaku iya mallaka makaman nukiliya ba. Idan kuma kuna so mu tattauna kofa na bude. In kuwa ba haka ba zaku ci gaba da fuskantar takunkuman tattalin arziki lokaci mai tsawo.

Manyan jami’an Amurka a kan tsaro da suka hada da mai bada shawara a kan tsaro John Bolton da mataimakin shugaban kasa Mike Pence sun yiwa Iran kashedi cewa kada ta dauki janyewa da Trump ya yi na maida martanin soja a kan harbe jiragen Amurka mara matuka a yankin tekun Hormuz a matsayin rauni daga Amurka.

Facebook Forum

XS
SM
MD
LG