Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Trump Ya Gargadi Putin Kan Katsalandan A Zaben Amurka


Shugaban Amurka Donald Trump, ya yiwa shugaban Rasha, Vladimir Putin, wani gargadi da kada ya kuskura ya sake yin shisshigi a cikin harkokin da suka shafi zaben Amurka.

Yayin da yake ganawa da manema labarai tare da Putin a gefe guda a taron da ake yi na kasashe masu karfin tattalin arziki na duniya, da akewa lakabi da G-20 a birnin Osaka na kasar Japan. An tambayi Trump ko zai gayawa shugaban kasar Rasha da kada ya kuskura ya sake katsalandan a cikin harkokin zaben Amurka?

Sai dai lokacin da Trump yake bada amsa a lokacin yace Eh, tabbas zan tambaye shi, yana kuma murmushi a fuskarsa, zan gayawa shugaban Rasha cewa “kada ka sake yi mana shisshigi a harkar zaben mu. Ya kuma sake maimaitawa kadaka sake yi mana shisshigi a harkar zabenmu, yayin da ya nuna dan yatsa ga Putin.

Wannan musayar akwai yuwuwar ta kara janyo shakku a cikin zukatan mutane da dama da suke ganin cewa Trump bai dauki abun da muhimmanci ba.

Wannan ce haduwa ta farko a tsakanin shuwagabanni tun lokacin da kwamitin bincike na musamman na Robert Mueller ya kammala rahotonsa, inda yace babu hadin bakin ko kuma hadin kai tsakanin kwamitin yakin neman zaben Trump, na shekarar 2016 da kuma jami’an gwamnatin Rasha.

  • 16x9 Image

    Yusuf Harande

    Yusuf Aliyu Harande, dan jarida da ke aiki da Sashen Hausa na Muryar Amurka (VOA). Yana da kwarewa a fannoni da dama, da suka hada da shafukan yanar gizo, talabijin, bincike, rubutu da hotuna. Dan asalin kauyen Hiliya ne daga karamar Hukumar Tambuwar a jihar Sakkwato.

Facebook Forum

XS
SM
MD
LG