Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Trump Ya Isa Taron Tattalin Arziki Na Duniya a Birnin Davos


Shugaban Amurka, Donald Trump

Shugaban Kasashen duniya sun hallara a birnin Davos da ke kasar Switzerland domin halartar taron tattalin arzikin na duniya.

Shugaban Kasar Amurka Donald Trump ya isa birnin Davos da ke Switzerland domin halartar taron tattalin arzikin na duniya.

Trump zai kasance shugaban Amurka na farko da ya halarci taron sanda yake kan mulki bayan ahugaba Bill Clinton da ya je a 2000.

Manazarta sun ce wakilai da yawa sun daura damarar jan daga akan sabanin ra’ayoyinsu kan yadda kowannensu ke kallon halin da tattalin arzikin duniya yake ciki.

Ana sa ran cewa Shugaba Trump zai yi kokarin tallata akidarsa ta maida Amurka ta farko, wanda ya sa Amurka ta saka haraji kan kayayyakin da ake shiga da su cikinta.

Sannan Amurka za ta nemi ta sauya tsarin cinikayyarta da sauran kasashen duniya.

Amma sauran manyan kasashen duniya kamar na nahiyar Turai da China da Japan, na kira da a sake sabon tsari na sassauta matakan kasuwanci tsakanin kasashe.

Facebook Forum

Laftanar Janar Farouk Yahaya

Makasan Sheikh Goni Aisami Sun Bata Sunan Sojin Najeriya – Laftanar Janar Farouk Yahaya
please wait

No media source currently available

0:00 0:02:11 0:00
Karin bayani akan Bidiyo

Shin da gaske NNPP ba ta yi wa Shekarau adalci ba?

Karin bayani akan Bidiyo
XS
SM
MD
LG