WASHINGTON D.C. —
Shugaban Amurka, Donald Trump, ya ce zai jinkirta bayar da jawabinsa game da “Halin da Kasa ke ciki” na wannan shekarar, har sai bayan da shi da Majalisar dokoki sun warware rikicin da ya kai ga rufe ma’aikatun gwamnatin tarayya.
Ba na neman wata hanya daban ta gabatar da wannan jawabin illa a majalisar dokokin, saboda babu wata hanya da za ta yi gasa da tarihi, al'ada da muhimmancin majalisar
A jiya Laraba ne Trump ya yi bayani a shafinsa na twitter cewar "Ba na neman wata hanya daban ta gabatar da wannan jawabin, illa a majalisar dokokin,saboda babu wata hanya da za ta yi gasa da tarihi, al'ada da muhimmancin majalisar.”
Da farko Jami'an Fadar White House sun ce sun fara neman wasu wurare na daban na gabatar da wannan jawabin, wadanda suka hada har da a gaban wani gangamin taron lacca, amma sun ce abin zai danganta ne akan ko dakatarwar ma’aikatun gwamnatin din za ta ci gaba.
Za ku iya son wannan ma
-
Janairu 25, 2023
Mawakiya Yar Najeriya Ta Yi Tarihi A Bikin Bada Lambar Yabo Na Oscar
-
Janairu 13, 2023
Lisa Marie Presley, Diyar Mawaki Elvis Ta Rasu
-
Janairu 11, 2023
Ana Tsaftace Yankunan Da Mahaukaciyar Guguwa Ta Ratsa A California
Facebook Forum