Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Trump Ya Nemi Rasha Ta Fice Daga Venezuela


Shugaba Donald Trump tare da uwargidan shugaban 'yan adawan venezuela (Juan Guaido) Fabiana Rosales a Washington, ranar 7 Maris, 2019.

A lokacin da manema labarai suka tambayi Trump ko yana duba yiwuwar shi ma ya tura dakarun Amurkan zuwa kasar ta Venezuela sai ya ce, “Amurka za ta iya amfani da kowanne irin zabi.”

Bayan da Rasha ta tura dakarunta zuwa kasar Venezuela, Shugaban Amurka Donald Trump ya aikawa da Rashan wani gargadi

Ya zama dole Rasha ta fice.Inji shugaba Trump.

Shugaban na Amurka ya yi wannan furuci ce ne, yayin da yake ganawa da manema labarai a Fadar White House a jiya Laraba, a lokacin da yake karbar bakuncin uwargidan shugaban ‘yan adawan kasar ta Venezuela, Fabiana Rosales.

A lokacin da manema labarai suka tambayi Trump ko yana duba yiwuwar shi ma ya tura dakarun Amurkan zuwa kasar ta Venezuela sai ya ce, Amurka za ta iya amfani da kowanne irin zabi.”

Yayin da take na ta jawabin, uwargidan Juan Guaido, wacce ta shiga har cikin ofishin shugaban kasa na Oval Office, ta ce jama’ar kasar ta Venezuela na cikin mawuyacin hali na rayuwa, musamman ma kananan yara.

Facebook Forum

Sakataren Gwamnatin kasar Amurka Michael R. Pompeo

Magoya Bayan Trump Sun Afkawa Ginin Majalisun Amurka

Magoya Bayan Shugaba Donald Trump Sun Mamaye Ginin Majalisar Dokokin Amurka
please wait

No media source currently available

0:00 0:00:56 0:00

Rayuwar Birni

Rayuwar Birni: Hira da Aliyu Danlami mai sayar da furanni a Abuja
please wait

No media source currently available

0:00 0:04:49 0:00
Karin bayani akan Rayuwar Birni
XS
SM
MD
LG