Shugaban Amurka Donald Trump, ya ce a shirye yake ya sake haduwa da takwaran aikinsa na Korea ta Arewa, Kim Jong Un, a yankin da babu dakaru, wanda ya raba Koriyoyi biyu, domin su gaisa.
Trump ya bayyana hakan ne a wani sakon Twitter da ya wallafa, gabanin ya sauka Korea ta Kudu a yau Asabar.
Yayin da yake ganawa da manema labarai a gefen taron G20 na kasashen da suka fi karfin tattalin arziki a Japan, Trump ya ce haduwar ta su ba za ta wuce ta minti biyu ba.
Shi dai Shugaba Kim bai ce komai ba dangane da wannan goron gayyata na na Trump, yayin da fadar gwamnatin Korea ta Kudu, ta ce, ba a cimma wata matsaya ba kan haduwar shugabannin biyu, inda ta ce tana fatan za a ci gaba da tattaunawa.
Ana dai fatan, wata sabuwar ganawa tsakanin Trump da Kim, za ta taimaka wajen farfado da tattaunawar da ake yi kan batun nukiliyan kasra ta Korea ta Arewa.
Za ku iya son wannan ma
-
Mayu 26, 2023
An Yi Girgizar Kasa Mai Karfi A Gabashin Japan
-
Mayu 25, 2023
Tina Turner, ta rasu tana da shekara 83
-
Mayu 19, 2023
Babban Taron Kungiyar Kasashen Larabawa A Saudiyya