Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Trump Ya Sauya Ra'ayinsa Akan Ba Malaman Makaranta Izinin Rike Bindigogi


Donald Trump shugaban Amurka

Jiay Alhamis Shugaban Amurka Donald Trump ya sake ra'ayinsa akan mallakar bindiga a makarantu inda yanzu yana son kashi 20 zuwa 40 na malaman makarantu su samu horo na musamman kana su fara rike bindigogi

A jiya Alhamis ne Shugaban Amurka Donald Trump ya sake ra’ayin sa game da yadda za a mallaki bindiga a makarantu.

Yace yana so ya zamanto kashi 20 zuwa 40 na malaman makaranta da suka samu horaswa sosai ne kawai zasu mallaki bindiga a boye cikin makarantu domin dakushe irin hare-haren da ake kaiwa a makarantu.

A lokacin da yake amsa wata tambayar VOA a karshen wani taron tattaunawar mintoci 55 akan irin yadda ake harbe-harbe a makarantu, a fadarsa ta White House, shugaba Trump yace, "malaman da suke so ne kawai za a ba bindigar. Kashi kadan kawai cikinsu zasu samu, amma suna da yawa. Da zarar an yi haka, nan take irin wannan bala'in zai kawo karshe."

Trump yace daga yanzu zai tabbatar sai an gudanar da binciken kwa-kwaf ga duk wani wanda zai sayi bindiga, haka kuma za a daga shekarun mallakar ta daga shekaru 18 zuwa 21, sannan za a haramta sayar da wani irin inji da ake makalawa jikin bindiga domin kara mata saurin fitar da harsasai.

Yace ba shakka muna son mu tabbatar cewa anyi wani abu game da wannan lamari, Shugaban na Amurka ya fadawa jami'an gwamnati dama sauran jama'ar gari haka ne sailin ganawar da yayi da su a fadar White House ta gwamnatin Amurka yace ba abinda yafi kare yaran mu muhimmanci.

A cikin sakonsa na farko a shafin Twiter shugaba Trump yace muddin aka horas da wasu malamai yadda zasu sarrafa bindiga, wannan zai basu damar mayar da martani nan take ga masu mummunar tabi'ar kai hari a cikin makaranta, haka kuma wannan zai zamo wata hanyar samar da tsaro.

Facebook Forum

Laftanar Janar Farouk Yahaya

Makasan Sheikh Goni Aisami Sun Bata Sunan Sojin Najeriya – Laftanar Janar Farouk Yahaya
please wait

No media source currently available

0:00 0:02:11 0:00
Karin bayani akan Bidiyo

Shin da gaske NNPP ba ta yi wa Shekarau adalci ba?

Karin bayani akan Bidiyo
XS
SM
MD
LG