Shugaban Amurka Donald Trump, ya kai ziyara kan iyakar kasar Mexico, inda jami’an tsaron Amurka suke sintiri a tashar da ake kira Calexico, domin sa ido kan masu shiga kasar ba bisa ka’ida ba.
Yayin ziyarar, shugaba Trump ya yabi irin ci gaban da ya ce ana samu, wajen dakile kwararar jama’a zuwa cikin Amurka.
Trump ya yi wadannan kalamai ne a wani daki da ke cke da jami’an da ke sintiri akan iyakar Amurka, da ‘yan majalisar wakilai da kuma wasu jami’an gwamnatinsa.
A baya-bayan nan, shugaba Trump ya yi barazanar rufe kudancin iyakar kasar da Mexico, ko da ya yi wasu kalamai da wasu ke ganin tamkar ya yi amai ya lashe ne
“A gaskiyar magana, sassaucin da zan iya idan ban rufe kan iyakar ba, shi ne a rika saka haraji ga motocin da ke shigowa, kuma zan yi hakan, kuma kun san zan aikata domin ni bana wasa.”
Trump ya kara da cewa, abubu biyu ne suke sa mutane suke tururwar zuwa Amurka, na farko shi ne domin sun ga kasar ta ci gaba, sannan wasu kuma suna zuwa ne domin su zo su yi damfara.
Facebook Forum