Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Trump Ya Yi Watsi Da Yarjejeniyar Makamai

Lokacin da shugaba Trump a lokacin da ya saka hannu kan wata doka da ta fitar da Amurkja daga yarjejeniyar makamai ta Majalisar Dinkin Duniya
Lokacin da shugaba Trump a lokacin da ya saka hannu kan wata doka da ta fitar da Amurkja daga yarjejeniyar makamai ta Majalisar Dinkin Duniya

Trump ya yi kira ga ‘yan majalisar dokokin kasar, da su daina sabunta wannan yarjejeniya, inda ya nemi da su dawo mai da ita, domin ya jefa ta a shara.

Shugaban Amurka Donald Trump, ya rattaba hannu akan wata takarda da ta yi watsi da shirin/yarjeniyar nan da ke sa ido kan cinikayyar makamai a tsakanin kasashe, wacce Majalisar Dinkin Duniya ke kula da shi, inda ya kwatanta shi a matsayin barazana ga Amurka, wacce ya ce kasa ce mai cin gashin kanta.

Shugaba Trump ya bayyana hakan ne a gaban dubban jama’a a Indianapolis, yayin da yake jawabi a taron kungiyar nan mai kare muradun masu mallakar bindiga a Amurka ta National Rifle Association ko kuma NRA a takaice, taron wanda ake yi shekara-shekara.

Trump ya yi kira ga ‘yan majalisar dokokin kasar, da su daina sabunta wannan yarjejeniya, inda ya nemi da su dawo mai da ita, domin ya jefa ta a shara.

Jawabin na shugaba Trump, ya farantawa mahalarta wannan taro rai, inda har jama’a suka tashi tsaye domin yi masa jinjina ta musamman.

“Gwamnatita, ba za ta taba saka hannun a wannan yarjejeniya ba ta cinikayyar makamai da Majalisar Dinkin Duniya ke sa ido akai ba.”
Sai dai masu goyon bayan wannan yarjejeniya ta cinikayyar makamai, sun ce, shirin ba ya wata barazana ga hakkin mallakar bindiga da doka ta bai wa Amurkawa.

Facebook Forum

XS
SM
MD
LG