Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Tsananin Sanyin Hunturu A Yakin Sahel Ya Kawowa Yara Cututtuka


Wasu mata da suka kawo 'ya'yansu jinya
Wasu mata da suka kawo 'ya'yansu jinya

Sanadiyar tsananin sanyin hunturu a yankin Sahel uwaye mata suna kwararawa da 'ya'yansu zuwa asibitoci a birnin Agadez saboda cututtuka da suka kamu dasu.

Sanyin ya kawo ciwon taushe nunfashin ma yara kanana a birnin Agadez lamarin da ya kada uwaye mata dangane da halin da 'ya'yansu suka shiga.

Wata da aka zanta da ita tace yaronta ne sanyin ya kamashi har ma wai basu samu sunyi barci ba. Sanyin ya rike mashi kirji sai da aka yi mashi masaji ko tausa.

Wata kuma sanyin ya haddasawa danta karancin jini saboda haka dole suka taso daga garin da suke zuwa Agadez domin neman magani.

Adadin yaran da suka kamu da ciwon a wannan shekarar ya zarce na shekarun baya. To amma likitoci sun ce rashin kulawa ta iyayen ke haddasa matsalar.

Madam Ibrahim Ramatu malamar babban asibitin Agadez ta lissafa akalalla cututtuka uku da yawancin yaran ke fama dasu.

Malaman asibitin suna bada magunguna kyauta tare da fadakar da kawunan iyaye mata dangane da matakan da suka dace su dauka domin yin rigakafi.

Ga rahoton Haruna Mamman Barma da karin bayani.

please wait

No media source currently available

0:00 0:02:30 0:00

Hawan Nasarawa, jihar Kano a Najeriya, lokacin da aka gudanar da bukukuwan Sallar Eid el Fitr
please wait

No media source currently available

0:00 0:03:44 0:00
Karin bayani akan Rahotannin Taskar VOA
XS
SM
MD
LG