Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Tsananin Zafi Ya Halaka Mutum Shida a Amurka


wani mutum yana watsa ruwa a fuskarsa saboda tsananin zafi a Amurka
wani mutum yana watsa ruwa a fuskarsa saboda tsananin zafi a Amurka

Kafofin yada labarai da dama, sun ce an samu mace-macen ne a jihohin Maryland, Arizona da Arkansas.

Jami'an lafiya a nan Amurka, sun ce tsananin zafin da ya mamaye wasu yankunan kasar, ya taimaka wajen mutuwar mutum akalla shida.

Kafofin yada labarai da dama, sun ce an samu mace-macen ne a jihohin Maryland, Arizona da Arkansas.

A jiya Asabar, hukumar kula da yanayi ta Amurka, ta yi gargadin cewa, za a fuskanci matsanancin zafi mai cike da hadari a wannan karshen makon da ake ciki, wanda zai iya haifar da matsananciyar gajiya da za ta sa har mutum ya fita a hayyacinsa, muddin mutane ba su bi matakan da suka dace ba.

Hukumomin sun ta kuma ba da shawara ga ‘yan uwa da makwabta da abokanai, da su rika duba halin da junansu ke ciki, musamman ma gajiyayyu da ke zaune a daki ba sa iya fita, domin sanin halin da suke cike.

A birane, hukumoki kuma ta ba da umurnin a bar tafkunan ninkaya ko kuma swimming pool su kasance a bude na tsawon lokutan da suka dara na da, tare da aikewa da sakonnin matakan da mutane ya kamata su dauka domin magance wannan zafi mai tsanani, inda a nan Washington, zai kai maki 38, a New York maki 33 duk a mataki na ma’aunin Celcius.

Facebook Forum

Hawan Nasarawa, jihar Kano a Najeriya, lokacin da aka gudanar da bukukuwan Sallar Eid el Fitr
please wait

No media source currently available

0:00 0:03:44 0:00
Karin bayani akan Rahotannin Taskar VOA
XS
SM
MD
LG