Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Tsare Mutane Ba Shari’a Baya Bisa Ka’ida – inji Barrister Dalung


Sojoji suna sintiri

Jama’a da dama da kwararru sun yi tambayoyi da yawa akan abunda ya faru Lahadinnan a shedkwatar ‘yan sandan sirri dake birnin tarayya Abuja.

Jama’a da dama da kwararru sun yi tambayoyi da yawa akan abunda ya faru jiya a shedkwatar ‘yan sandan sirri dake birnin tarayya Abuja, wanda yake da wajen tsare mutane a cikinsa.

Amma abun lura shine hare-hare akan wuraren da ake ajje masu laifi na karuwa, idan akayi la’akari da misali barikin Giwa dake birnin Maiduguri a baya-bayannan.

Saboda haka, tambayar anan itace meyasa ake kai wadannan hare-hare a gidajen kaso? Kuma yayi dai-dai a ka’idance a ajje mutane da ake zargi da laifi ba tare da gurfanar da su a gaban shari’a ba?

Kwararre mai fashin baki akan harkokin shari’a, tsaro da siyasa, Barrister Solomon Dalung yayi fashin baki akan wannan lamarin.

Dalung yace "kama masu tayar da kayar baya a Najeriya da tsaresu a barikin sojoji, da ofisoshin 'yan sanda ciki ba dai-dai bane, abinda ya kamata shine a gurfanar dasu a gaban kotu, ayi masu hukumcin da doka ta tanada, da kuma kaisu gidajen yari."

Ya kara da cewa tsare irin wadannan mutane a barikin sojoji da kuma ofisoshin jami’an tsaro bai dace ba, domin shine yake kawo kokarin da ‘yan uwansu suke yi na kokarin kubutar dasu.
please wait

No media source currently available

0:00 0:07:52 0:00
Shiga Kai Tsaye
XS
SM
MD
LG