Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Tsofaffin Jami’an ‘Yan Sandan Najeriya Sun Koka


Sifeta janar na 'yan sandan Najeriya, Mr. Solomon Arase
Sifeta janar na 'yan sandan Najeriya, Mr. Solomon Arase

Kungiyar tsofaffin ‘yan sanda a Najeriya ta bukaci gwamnatin tarayya da ta duba tsarin biyan kudin sallama da fenshon ‘ya‘yanta domin su sami rayuwa mai inganci.

A wani gagarumin taron da tsofaffin ‘yan sandan suka gudanar daga dukan jihohin tarayyar Najeriya a Jos fadar gwamnatin jihar Plato, sun koka kan yadda wadansu kamfanonin da aka ba kwangilar biyansu kudin fensho ke wulakantasu kafin biyansu kudin da bai taka kara ya karya ba.

Sakataren kungiyar tsofaffin ‘yan sandan na kasa, ASP Silvanus T. Basadeimbo, yace sun yiwa Najeriya aiki na tsawon shekaru biyar, amma bayanda suka yi ritaya, abinda aka sallame su da shi bai taka kara ya karya ba. Yace shi kanshi kudin sallamar da aka bashi naira miliyan daya da dari uku ne kawai, yayinda kuma ake bashi naira dubu talatin da daya kawai fensho a wata.

Yace duk kokarin da suka yi na neman a yi gyara a tsarin, da ya hada da rubuta wasika zuwa majalisar dokoki ta tarayya amma aka yi watsi da su. Sabili da haka suke kira ga shugaban kasa ya taimaka masu.

Tsofaffin ‘yan sandan sun bayyana cewa, wani abinda ya dame su shine kamfanonin da aka ba suna biyan kudaden suna danne kudaden su rika gutsurar masu wata wata. Suka bayyana cewa, abinda suke bukata shine, a basu kudadensu duka su zabi yadda zasu sarrafa kudinsu da kansu.

Ga cikakken rahoton da wakiliyarmu Zainab Babaji ta hada mana.

Tsofaffin 'Yansandan Najeriya-3:54'
please wait

No media source currently available

0:00 0:03:54 0:00
Shiga Kai Tsaye

  • 16x9 Image

    Grace Alheri Abdu

    Grace Alheri Abdu  babbar Edita ce (Managing Editor) a Sashen Hausa na Muryar Amurka wadda ta shafe sama da shekaru 30 tana aikin jarida. Tana da digiri na biyu a fannin dokoki da huldar diplomasiyar kasa da kasa, da kuma digiri na biyu a fannin nazarin addinan al'adun gargadiya na kasashen Afrika.

XS
SM
MD
LG