Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Tsohon Gwamnan Jihar Gombe Habu Hashidu Ya Rasu


Tsohon gwamnan jihar Gombe Abubakar Habu Hashidu
Tsohon gwamnan jihar Gombe Abubakar Habu Hashidu

Marigayi Alhaji Habu Hashidu, wanda Allah ya yi wa rasuwa a ranar Juma'a ya taba rike mukamin ministan albarkatun ruwa da kuma ministan ayyukan gona da bunkasa yankunan karkara a zamanin mulkin soja na shugaba Ibrahim Babangida inda daga nan ne ya yi ritaya.

Tsohon gwamnan jihar Gombe, Alhaji Habu Hashidu ya rasu bayan fama da ya yi da rashin lafiya.

Ya rasu yana mai shekaru 74.

An yi jana'izar marigayin a kofar fadar sarkin Gombe da misalin karfe 5 na yamma a yau Juma'a 27 ga watan Yulin shekarar 2018.

An haife shi a garin Hashidu da ke karamar hukumar Dukku a jihar ta Gombe a ranar 10 ga watan Afrilun shekarar 1944.

Marigayin ya yi ayyuka da dama a zamanin tsohuwar gwamnatin jihar arewa maso gabas a ma'aikatar gona da albarkatun kasa, a yayin da ya taba rike mukamin kwamishinan ayyukan gona a tsohuwar gwamnatin jihar Bauchi.

Har ila yau taba rike mukamin ministan albarkatun ruwa da kuma ministan ayyukan gona da bunkasa yankunan karkara a mulkin soja na shugaba Ibrahim Babangida inda daga nan ne ya yi ritaya.

A shekarar 1999 marigayi ya yi takarar kujerar gwamnan jihar gombe a karkashin jam'iyar APP ta da inda ya yi mulki daga shekarar 1999 zuwa 2003.

Habu Hashisu ya rasu ya bar mata daya da yara takwas maza uku mata biyar.

  • 16x9 Image

    Grace Alheri Abdu

    Grace Alheri Abdu  babbar Edita ce (Managing Editor) a Sashen Hausa na Muryar Amurka wadda ta shafe sama da shekaru 30 tana aikin jarida. Tana da digiri na biyu a fannin dokoki da huldar diplomasiyar kasa da kasa, da kuma digiri na biyu a fannin nazarin addinan al'adun gargadiya na kasashen Afrika.

Facebook Forum

XS
SM
MD
LG