Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Tsohon Gwamnan Jihar Osun Sanata Isiyaka Adeleke Ya Rasu


Sanata Isiyaka Adeleke, tsohon gwamnan jihar Osun

Jiya Lahadi da yamma ne Sanata Isiyaka Adeleke ya fara nuna zazzabi a garinsa Ede nan take kuma a garzaya dashi asibiti a garin Oshogbo babban birnin jihar inda rai yayi halinsa

An haifi Sanata Isiyaka Adeleke a Enugu ranar 15 ga watan Janairu na shekarar 1955.

Shi dai Sanata Adeleke ya karanta digiri na farko da na biyu a fannin mulkin jama'a.

Sanata Isiyaka Adeleke tsohon gwamnan Osun yayinda yake fafutikar neman zabe a karkashin jam'iyyar APC
Sanata Isiyaka Adeleke tsohon gwamnan Osun yayinda yake fafutikar neman zabe a karkashin jam'iyyar APC

A lokacin rayuwarsa marigayin ya rike mukamai da dama.

Mazauna jihar Osun sun nuna juyayi bisa ga rasuwar Sanata Isiyaka Adeleke. Suna mai cewa sun yi rashi babba. Sun ce mutum ne nagari saboda yayi abubuwan cigaba.

Ga rahoton Hassan Umaru Tambuwal da karin bayani.

please wait

No media source currently available

0:00 0:01:52 0:00

Facebook Forum

XS
SM
MD
LG