Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Tsohon kakakin majalisar wakilan Najeriya ya musanta aikata zarmiya


Yan sandan Najeriya

Tsohon kakakin Majalisar wakilai ta tarayya yaki amsa laifin tuhuma da ake maza na sama da fadi da miliyoyin dala na kudaden majalisa

Tsohon kakakin Majalisar wakilai ta tarayya yaki amsa laifin tuhuma da ake mashi na sama da fadi da miliyoyin dala na kudaden majalisa. Yau laraba aka gurfanar da Dimeji Bankola a gaban wata babban kotun Abuja kan zargin aikata laifuffuka daban daban har goma sha shida. Masu gabatar da kara sunce zasu gabatar da karin caje caje kan tsohon kakakin. Kotun ta bada umurnin a ci gaba da tsare Mr. Bankole har zuwa jumma’a, ranar da za’a saurari bukatar beli daya gabatar. Hukumar yaki da cin hanci da rashawa ta Najeriya (EFCC) tana zargin Mr. Bankole da kara farashin komputoci da printers, da akwatunan talabijin, da kuma na motocin shakatawa na majalisar.Hukumar tace tana jin Mr. Bankole ya saci akalla dala miliyan sittin.

Shin PI Za Ta Fashe Kuwa Ko Yaudara Ce Kawai?

Karin bayani akan Bidiyo
XS
SM
MD
LG