Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Tsohon Ma'aikacin Sashen Hausa Ladan Ibrahim Ayawa Ya Rasu


LADAN IBRAHIM AYAWA

Ladan Ibrahim Ayawa ya rasu a asibitin George Washington dake birnin Washington, DC, bayan gajerar jinya.

Kafin rasuwarshi, Ladan Ibrahim Ayawa ya yi aiki da Muryar Amurka na tsawon shekaru da dama, inda ya fara a matsayin wakili da ke dauko rahotanni a birnin Lagos, kafin a dauke shi aiki a shelkwatar Sashen Hausa a Washington.

Marigayi Ladan Ibrahim Ayawa wanda haifaffen jihar Naija ne, kwararren dan jarida ne wanda kafin aiki da Muryar Amurka, ya kuma yi aiki da Radio Nigeria.

Daga cikin fitattun shirye shiryen da Ladan ya gabatar akwai shirin Himma bata ga rago, shirin da ke hira da 'yan asalin kasar Afrika dake zaune a kasashen ketare.

Himma Bata ga rago-6:00"
please wait
Embed

No media source currently available

0:00 0:07:32 0:00


Ladan Ayawa ya kuma gabatar da shirin da ke haska fitila kan harkokin zabe a kasashen duniya musamman kasashe masu tasowa inda ake yawan zargin magudi.

Ga shirin Zabe ko nadi na karshe da ya gabatar

Zabe Ko nadi-13:00"
please wait
Embed

No media source currently available

0:00 0:13:31 0:00

Ladan ya rasu ya bar matarsa Talatu da kuma 'ya'ya uku, namiji daya da 'yammata biyu.

Yau ake kyautata zaton za a yi jana'izar shi a jihar Maryland bayan an yi mashi sallah a babban masallacin karamar Hukumar Prince Georges.

Facebook Forum

XS
SM
MD
LG