Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Tsohon Mataimakin Gwamnan Kaduna Barnabas “Bantex” Ya Rasu


Marigayi tsohon mataimakin gwamnan jihar Kaduna Barnabas Bantex (Facebook/El Rufai).
Marigayi tsohon mataimakin gwamnan jihar Kaduna Barnabas Bantex (Facebook/El Rufai).

“Bantex mutum ne mai basira, tare muka dauki ragamar samar da shugabanci na gari a jihar Kaduna a shekarar 2015.” In ji El Rufai.

Gwamnatin jihar Kaduna ta sanar da mutuwar tsohon mataimakin gwamna Barnabas Yusuf Bala wanda aka fo sani da Bantex.

Cikin wata sanarwa da ya fitar, gwamna Malam Nasiru El Rufai ya nuna kaduwarsa dangane da jin labarin rasuwar tsohon mataimakinsa, wanda ya rike mukamin tsakani watan Mayun 2015 zuwa watan Mayun 2019.

Bantex mutum ne mai basira, tare muka dauki ragamar samar da shugabanci na gari a jihar Kaduna a shekarar 2015.” In ji El Rufai.

Karin bayani akan: Nasiru El Rufai, Yusuf Bala, jihar Kaduna, Nigeria, da Najeriya.

Baya ga mukamin mataimakin gwamna, Bantex ya rike mukamai da dama, ciki har da zama wakili a taron sauya fasalin kundin tsarin mulkin Najeriya a shekarar 1994, shugaban karamar hukumar Kaura sannan ya taba wakiltar mazabar Kaura a majajisar wakilai ta tayarra a cewar sanarwar.

“Za mu yi matukar kewar basirarsa da irin himmarsa wajen yi wa jihar Kaduna hidima, da kuma saukin kansa da kasancewarsa mutum mai barkwanci.”

Cikin sanarwar wacce ya tuno da yadda suka yi karatun jami’a tare da marigayin, gwamna El Rufai ya kuma ce tuni ya mika ta’aziyyarsa ga iyalan marigayin.

“Za mu yi aiki tare da iyalansa domin a masa jana’izar karramawa, ga wannan mutum da ya sadaukarsa da kansa ga jiharsa duk da fama da jinya da yake yi” a lokacin yana raye.

Gwamnatin jihar Kaduna ta ayyana ranar Fitinin 12 ga Watan Yuli a matsayin ranar hutu don jimamin rasuwar Bantex.

XS
SM
MD
LG