Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Tsohon Shugaba Gowon Ya Jagoranci Addu’a Ta Musamman Ga Buhari


Tsohon Shugaban Najeriya Janar Yakubu Gowon Da Wakilin Muryar Amurka Ibrahim Abdul'aiziz
Tsohon Shugaban Najeriya Janar Yakubu Gowon Da Wakilin Muryar Amurka Ibrahim Abdul'aiziz

Yayin da ‘yan Najeriya ke ci gaba da yiwa shugaban kasa Muhammadu Buhari addu’ar samun lafiya, tsohon shugaban kasar Janar Yakubu Gowon, ya nuna damuwarsa game da yadda ake saka siyasa a rashin lafiyar shugaban ‘kasa.

Gowon wanda ya jagoranci addu’o’i na musamman don ci gaban Najeriya, a jahar Adamawa, ya bukaci yan ‘kasar musamman yan siyasa da suke karatun ta natsu domin ciyar da kasar gaba.

A cewar tsohon shugaban shima lokacin da yake kan mulki yayi rashin lafiya, kuma hakan ba wani abu bane na damuwa domin kowa kan iya kamuwa da rashin lafiya a kowanne lokaci.

Gowon ya kuma yi kira ga duk ‘yan Najeiya da a ci gaba da yiwa shugaban addu’a, duk da yake likitoci suna bashi kulawar da ta kamata, da kuma gujewa cece-kuce irin na siyasa.

Sai dai kuma wannan ziyarar addu’oin da tsohon shugaban kasar ya jagoranta na zuwa ne yayin da hadakar kungiyar magoya bayan Buhari da Osinbajo ta BOA, ke gudanar da gangamin addu’o’a a Yola, inda aka yi wa shugaba Buhari addu’a ta musamman.

Dan Majalisar Dokokin jihar Adamawa, Rufai Gombi, na daga cikin shugabanin kungiyar BOA, yace sun shirya taron gangamin addu’ar ne don rokon Allah ya baiwa shugaban lafiya ganin ayyukan da aka fara musamman a jahohin Arewa maso Gabashin kasar.

Ya zuwa yanzu dai ana cigaba da gudanar da irin wadannan addu’o’i ga shugaba Buhari a wasu sassan Najeriya.

Domin karin bayani ga rahotan Ibrahim Abdul'aziz.

please wait

No media source currently available

0:00 0:03:53 0:00

Facebook Forum

XS
SM
MD
LG