Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Tsohon Shugaban Mulkin Soja Zai Tsaya Takara a Nijar


Taron jam'iyyar PJP a Nijar
Taron jam'iyyar PJP a Nijar

A jamhuriyar Nijar sabuwar jam’iyar PJP Generation Dubara ta bayyana tsohon shugaban gwamnatin mulkin soja Janar Salou Djibo a matsayin wanda zai tsaya mata takara a zaben shugaban kasa na watan disambar 2020.

Taron jam’iyar na kasa wanda ya gudana a tsawon wunin jiya Lahadi ne ya zabi Janar Salou Djibo a matsayin dan takararta.

Taron jam'iyyar PJP a Nijar
Taron jam'iyyar PJP a Nijar

A cewar Djibo lura da tarin matsalolin da kasa ke fama da su kamar cin hanci da rashin hukunta masu laifuka da siyasar raba kawunan ‘yan kasa ya sa shi yanke shawarar shiga fagen siyasa domin tayarda komada.

Tsohon shugaban gwamnatin mulkin sojan ya sha alwashin kawo sauyi a sha’anin siyasa.

"Idan ‘yan Nijar suka zabe ni zan takaita yawan ministocin gwamnati sa'annan zan shimfida tsarin baiwa majalisar dokoki aikin tantance wadanda za a nada a manyan mukaman shugabanci."

"Daga yanzu har zuwa lokacin yakin neman zabe kawo lokacin da zamu lashe wannan zabe ba zan ci zarafi ko yiwa wani dan siyasa kazafi ba," a cewar Djibo.

Taron Jam'iyyar PJP a Nijar
Taron Jam'iyyar PJP a Nijar

Dan shekaru 55 a duniya, Djibou ya fara fito da sunansa ne a ranar 18 ga watan fabrairun 2010 lokacin da ya jagoranci sojojin da suka kifar da gwamnatin shugaba Tanja Mamadou daga karagar mulki.

Bayan da ya shirya zaben da aka bayyana dan takarar PNDS TARAYYA, Issouhou Mahamadou a matsayin wanda ya yi nasara, janar Salou ya fara aiki da kungiyar ECOWAS.

Ya yi karatu a jami’ar Ahmadu Bello ta Zaria inda ya karanci kimiyar siyasa kafin daga bisani ya kafa jam’iyar PJP DUBARA a Bara.

Facebook Forum

Hawan Nasarawa, jihar Kano a Najeriya, lokacin da aka gudanar da bukukuwan Sallar Eid el Fitr
please wait

No media source currently available

0:00 0:03:44 0:00
Karin bayani akan Rahotannin Taskar VOA
XS
SM
MD
LG