Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Tsokacin ‘Yan Adamawa Game Da ‘Daure Tsohon Gwamnansu


ADAMAWA: Kotu ta daure Barrister Bala Ngilari, tsohon gwamnan jihar

Biyo bayan hukuncin da wata babbar kotu a jihar Adamawa ta yanke wa tsohon gwamnan jihar James Bala Ingilari, daurin shekaru biyar a gidan kaso saboda sabawa ka'idojin bayar da kwangila, yanzu haka al’umman jihar da kuma masana sharia na tsokaci.

ya ga James Ibori, Barista Bala James Ngillari yanzu shine gwamna na biyu da kotu ta daure bisa zargin cin hanci da rashawa ko keta ka’idar aiki tun bayan da Najeriya ta koma tafarkin dimokaradiyya a 1999, batun da masu sharhi akan al’amurra ke ganin wannan hukuncin yana da muhimmanci da hakan ka iya zama darasi nan gaba.

Yanzu haka dai wannan batu dai shine ya dauke hankulan mutane a ciki da wajen Yola fadar jihar Adamawa, kasancewar yanzu haka akwai sauran tsofaffin gwamnonin jihar biyu dake gaban kuliya game da zargin laifuffukan da suka shafi cin hanci da rashawa.

Mallam Umar Dankano dake zama mataimakin shugaban kungiyar yan jarida ta jihar Adamawa na ganin akwai abin dubawa.

Shima wani mai sharhi da fashin baki kuma malami a kwalejin kimiyya da fasaha ta jihar Mallam Lawan Danladi, yace kukan kurciya aka yi.

Kotun dai ta yanke wa tsohon gwamnan jihar ne Bala James Ngillari, hukuncin daurin shekaru biyar a gidan Yari, saboda sabawa ka’idojin bayar da kwangila batun da masanin shari’a Barista Sunday Joshua Wigra ke ganin akwai abin dubawa.

Domin karin bayani saurari rahotan Ibrahim Abdul’aziz.

please wait

No media source currently available

0:00 0:03:28 0:00

Facebook Forum

Sauyin yanayi : Yankin Sahel na Afrika

Yadda Sauyin Yanayi Ke Rura Wutar Rikici A Yankin Sahel
please wait

No media source currently available

0:00 0:12:44 0:00
Karin bayani akan Rahotannin Taskar VOA

Nijar, Fulani, Wodaabe

Yadda Funalin Wodaabe Suka Gudanar Da Gasar Nuna Kyau A Nijar
please wait

No media source currently available

0:00 0:02:22 0:00
Karin bayani akan Rahotannin Taskar VOA

Gobara A Jihar New York

An Yi Jana'izar Mutane 15 Da Suka Mutu A Gobara A Jihar New York
please wait

No media source currently available

0:00 0:03:00 0:00
Karin bayani akan Bidiyo
XS
SM
MD
LG