Accessibility links

Tsuguno Bai Kare Ba Game Da Kakakin Majalisar Dokokin Nijer Hama Amadou

  • Halima Djimrao

Kakakin Majalisar Dokokin kasar Nijer Hama Amadou.

Wata kotu ta gabatar da sammacin kama Hama Amadou.

Rikicin siyasa na ci gaba da kunno kai jiddin wala hairan a kasar jamahuriyar Nijer tun bayan zargin da aka yiwa kakakin majalisar dokoki Hama Amadou da iyalin shi cewa su na da hannu dumu-dumu a abun fallasar sayen jarirai daga kasar Najeriya.

Duk da cewa Hama Amadou ya bar kasar Nijer ya samu mafaka a kasar Faransa wata kotu ta gabatar da sammacin kamo shi, al'amarin da ya haifar da rudami, da jefe-jefen juna da kalamai marasa dadi tsakanin bangaren masu mulki da na magoya bayan Hama Amadou.

Wakilin Sashen Hausa a Niamey babban birnin kasar jamahuriyar Nijer Abdoulaye Mamane Amadou ya aiko rahoto akan wannan sabuwar badakala:

Hama Amadou ya bar kasar Nijer ne a lokacin da aka bukace shi ya bayyana a gaban wata kotu ya wanke kan shi daga zargin hannu a cikin abun fallasar sayen jarirai daga kasar Najeriya.

Wannan abun fallasar safarar jarirai ya rutsa da manyan jami'an kasar Nijer tare da iyalan su, a ciki har da ministan aikin gona Abdou Labo.

XS
SM
MD
LG