Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Tsuguno Fa Bai K'are Ba A Adamawa Game Da Neman Tsige Gwamna Murtala Nyako


Murtala Nyako, gwamnan Jihar Adamawa

Mukaddashin Cif Jojin jahar Adamawa Ambrose Mammadi ya kafa kwamitin mutum 7 kamar yadda majalisar jahar ta bukata.

Ga dukan alamu Majalisar Dokokin jahar Adamawa ta samu biyan bukatar ta, ta neman a kafa kwamitin da zai gudanar da binciken tabbatar da hujjojin tsige gwamnan jahar Murtala Nyako da Mataimakin shi Barrister Bala James Ngillari.

Bayan bukatar da majalisar ta gabatar a kwanakin baya, mukaddashin Cif Jojin jahar ta Adamawa Ambrose Mammadi ya kafa kwamitin mutane bakwai wanda zai gudanar da bincike a kan gwamnan jahar da mataimakin shi.

An kafa kwamitin binciken gwamna Murtala Nyako.-1':02"
please wait

No media source currently available

0:00 0:01:02 0:00
Shiga Kai Tsaye

Babban rajistara na babbar kotun jahar Adamawa, Abubakar M.Bayola ne ya sanya hannu a kan takardar sanarwar kafa kwamitin.

Mukaddashin Cif Jojin Ambrose Mammadi ya kafa wannan kwamiti ne a daidai lokacin da gwamna Murtala Nyako ke wanke gwamnatin tarayya daga zargin cewa ita ce ta kitsa kulle-kulle ta da kumbiya-kumbiyar tsige shi daga mukamin shi na gwamna.

Wakilin Sashen Hausa na Muryar Amurka a Jahohin Adamawa da Taraba, Ibrahim Abdulaziz ne ya aiko da rahoton.

XS
SM
MD
LG