Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Tun Shekarar 2011 Gwamnatin Jihar Bauchi Ba Ta Biya Tsoffin Ma'aikata Ba


Gwamnan Jihar Bauchi Barrister M. A. Abubakar

Duk da cewa gwamnatin tarayya ta taimakawa jihohi da kudin Paris Club har sau biyu domin biyan ma'aikata, gwamnatin jihar Bauchi ko kwandala ba ta biya ma'aikatanta ba lamarin da yanzu ya harzuka mutane har suna shirin zuwa yin zanga zanga

A yayinda wasu jihohin suka biya ma'aikatansu wasu kaso daga kudin da gwamnatin tarayya ta basu, wasu kuwa ko kwandala basu biya ba.

A jihar Bauchi tsoffin ma'aikata ba'a biyasu kudin barin aiki ba tun daga shekarar 2011 zuwa yanzu lamarin da ya sa wadanda abun ya shafa lasar takobin gudanar da zanga zanga.

Mai magana da yawun ma'aikatan yace akwai kudin da gwamnatin tarayya ta bayar sau biyu na Paris Club ma jihohi. Wasu sun bi umurnin gwamnatin tarayya sun biya amma Bauchi ta yi kunnen shegu. Wasu sun biya har zuwa shekarar 2016. Wasu ma sun gama biya har da na wannan shekarar.

Inji ma'aikatan a Bauchi wasunsu sun mutu ba su samu kudinsu ba. Saboda haka suna kiran gwamnati ta biyasu, ta yi adalci.

A cewar wani cikinsu basu da shugabanci kama daga kungiyar kwadago zuwa tasu ta tsoffin ma'aikata, sai dai wadanda suke aiki yanzu su ma watarana zasu bar aikin. Amma yanzu zasu shirya su je gidan gwamnati da majalisar dokoki domin su nuna bacin ransu.

Shugaban kungiyar masu karban fansho a jihar Alhaji Habu Gar yace sun gana da jami'an gwamnati kan batun kuma an cimma matsaya. Yanzu an kawo karshe kuma gwamnan yace a cigaba da biyan ma'aikatan daga 2011 zuwa wannan shekarar.

Ga rahoton Abdulwahab Muhammad da karin bayani.

please wait

No media source currently available

0:00 0:03:16 0:00

Facebook Forum

XS
SM
MD
LG