Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Tuna Baya: Juyin Mulkin Soja Na Farko A Najeriya


Daga ranar 15 zuwa 16 ga watan Janairun shekarar 1966, wasu kananan hafsoshin soja masu mukaman manjo sun aiwatar da juyin mulkin soja na farko wanda suka fara kitsawa tun a watan Agustar shekarar 1965.

Wadannan kananan hafsoshin soja, sun yi ikirarin cewa sun shirya juyin mulkin ne a saboda a cewarsu, shugabannin dake jagorancin kasar sun nuna zarmiya, inda suka ce ministocin gwamnati suna sace kudaden baitul-mali domin amfaninsu.

Sai dai kuma a wani bangare, akwai masu ikirarin cewa wannan juyin mulki na kabilanci ne a saboda daga cikin sojoji 8 da suka kulla wannan juyin mulki, guda 7 'yan kabilar Igbo ne, daya kuma Bayarbe. A wani gefen kuwa, dukkan manyan shugabannin farar hular da aka kashe, har ma da wasu manyan hafsoshin soja, kusan 'yan Arewacin Najeriya ne.

Wadanda suka shirya juyin mulkin, sune Manjo Chukwuma Nzeogwu wanda ke Kaduna a lokacin, wanda kuma shi ya jagoranci kashe Firimiyan Arewa, Sir Ahmadu Bello, Sardaunan Sokoto.

Manjo Emmanuel Ifeajuna, shine ya jagoranci juyin mulkin daga Lagos, kuma ya jagoranci kashe Firayim Minista Sir Abubakar Tafawa Balewa, da Birgediya Zakari Maimalari, wanda a lokacin shine hafsan soja mafi girma daga yankin Arewacin Najeriya.

Shugaban Kasa maras iko a lokacin, kuma dan kabilar Igbo, Nnamdi Azikiwe, ya bar kasar a lokacin da wadannan sojoji suka kaddamar da juyin mulkin.

A saboda Azikiwe ba ya cikin kasar, kuma an kashe firayim minista, sai mai rikon mukamin shugaban kasa a lokacin, Nwafor Orizu, shi ma dan kabilar Igbo, yayi jawabi ga kasa inda yace majalisar zartaswa ta yarda domin radin kanta, ta mika mulki ga sojoji.

Manjo-janar Aguiyi-Ironsi tare da gwamnonin da ya nada a larduna hudu na Najeriya. (hagu zuwa dama) Manjo Hassan Usman Katsina; sai leftana-kanar F. A. Fajudi; leftana-kanar Odumegwu Ojukwu; da leftana-kanar D. A. Ejoor
Manjo-janar Aguiyi-Ironsi tare da gwamnonin da ya nada a larduna hudu na Najeriya. (hagu zuwa dama) Manjo Hassan Usman Katsina; sai leftana-kanar F. A. Fajudi; leftana-kanar Odumegwu Ojukwu; da leftana-kanar D. A. Ejoor

Daga nan sai babban kwamandan sojojin Najeriya a lokacin, Manjo-janar Johnson Aguiyi-Ironsi, yayi jawabin cewa ya amshi ragamar mulki. A ranar 17 ga watan Janairu, sai ya bayyana kafa majalisar koli ta soja, ya kawo karshen mulkin dimokuradiyya a kasar.

Wadanda aka kashe a juyin mulkin na farko, sun hada da Firayim minista Abubakar Tafawa Balewa; Firimiyan Arewa, Ahmadu Bello; Firimiyan Yamma, Samuel Akintola; Ministan Kudi, Festus Okotie-Eboh (shine kadai dan yankin gabas a cikin gwamnatin tarayya da aka kashe); Ahmed Ben Musa; Birgediya Zakariya Maimalari; Birgediya Samuel Ademulegun; Kanar Kur Mohammed; Kanar Shodeinde; Laftanal-kanar Abogo largema; Laftanal-kanar James Pam da leftana-kanar Arthur Unegbe.

Shi ma Saje Daramola Oyegoke, an ce ya taimakawa Nzeogwu wajen kai hari a kan gidan Sardauna, amma a cewar 'yan sanda, daga baya Nzeogwu ya kashe shi.

A ranar 28 ga watan Yulin 1966, watanni shida bayan wannan juyin mulki, hafsoshin soja daga Arewacin Najeriya sun shirya suka kaddamar da nasu juyin mulkin, wanda ya kai ga kashe Janar Aguiyi-Ironsi tare da laftanal-kanar Adekunle Fajuyi.

Wadanda suka shirya wannan juyin mulki sune Laftanal-kanar Murtala Mohammed; laftanal-kanar Joseph Akahan; Manjo T.Y. Danjuma da dai sauran kananan hafsoshin sojan Arewacin najeriya cikinsu har da Laftanal Ibrahim Babangida da Laftanal Muhammadu Buhari.

Facebook Forum

XS
SM
MD
LG