Kasar Turkiya tace tana taimakawa Kurdawa, su tsalaka zuwa kasar Syria domin taimakon mayakan Kurdawa, a yayinda suke fafatawa da nufin tare yan yakin sa kan kungiyar daular Islama, kutsawa birin Kobani.
Ministan harkokin wajen Turkiya Mevlut Cavusoglu bai bada wani karin haske ba, a yayinda yake shedawa yan jarida wannan batu na taimakon mayakan Kurdawan a yau Litinin.
An dauki wannan mataki ne kwana daya bayan da shugaban Turkiya Recep Tayip Erdogan yace kasar sa ba zata baiwa mayakan Kurdawa taimakon makamai ba, a yayinda ya ce daidai suke da yan jam'iyar Kurdistan Workers, jam'iyar da Amurka da ita kanta kasar Turkiya suka dauke ta a zamar kungiyar 'yan ta'ada.
Haka kuma daukan wannan mataki ya biyo bayan jefo kakayaki da jiragen saman dakon kaya na Amurka suka yi a ranar Lahadi, lokacinda suka yi jigilar makamai da alburusai da kuma magunguna daga hukumomi Kurdawa a Iraq zuwa ga mayakan Kurdawa a Korbani kusa da kan iyakar Turkiya.
Manyan jami'ai sun fadawa yan jarida cewa a ranar Asabar shugaba Barack Obama na Amurka ya shedawa Mr Erdogan wannan aniya ta jefo kayayyaki a zantawar da suka yi.
WASHINGTON, DC —