Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

UEFA: Karawar Paris Saint Germain Da Real Madrid


Lokacin wata karawar PSG da Real Madrid a gasar UEFA a 2019

PSG na kokarin ganin ta kai ga matsayin lashe kofin gasar a karon farko yayin da Madrid take tunkaho da tarihin lashe gasar sau 13.

Paris Saint Germain da Real Madrid na shirin karawa a wasan farko na zagayen ‘yan 16 a gasar cin kofin nahiyar turai na UEFA ranar Talatar nan.

PSG na kokarin ganin ta kai ga matsayin lashe kofin gasar a karon farko yayin da Madrid take tunkaho da tarihin lashe kofin gasar har au 13.

Madrid, wacce ta lashe kofin Super Copa a wannan shekara, ba ta kai ga wasan karshe a gasar ta UEFA ba tun bayan 2018.

Ana sa ran PSG za ta fito da zakukuran ‘yan wasanta irinsu Lionel Messi, Kylian Mbappe, Angel Di Maria da Sergio Ramos da Neymar a wasan, wanda za a yi a zagayen na farko.

A bangaren Madrid, masu bibiyar kwallon kafa sun zuba ido su ga ko dan wasanta Karim Benzema wanda ya farfado daga jinya zai buga wasan.

Kwana 21 ya kwashe ba ya kwallo, hakan ya sa bai samu damar buga wasannin uku ba.

Za a buga wasan ne a Parc de Princes a birnin Paris da ke Faransa.

AFCON 2021, Troost-Ekong

Abin da kyaftin Troost-Ekong ya ce da Najeriya ta lashe wasanninta uku a jere bayan doke Guinea-Bissau
please wait

No media source currently available

0:00 0:02:15 0:00
Karin bayani akan AFCON 2021

AFCON 2021, Super Eagles

Yan wasan Najeriya na atisaye gabanin karawar da za su yi da Guinea-Bissau a rukunkin D na gasar AFCON
please wait

No media source currently available

0:00 0:01:08 0:00
Karin bayani akan AFCON 2021

AFCON 2021: Troost-Ekong

Kowa ya san cewa mun iya taka leda’ In ji Troost-Ekong, yayin da Najeriya ta kai zagayen knockouts
please wait

No media source currently available

0:00 0:01:03 0:00
Karin bayani akan AFCON 2021

AFCON 2021, Kelechi Iheanacho

"Ku doke daya daga cikin shahararrun koci a duniya", Kelechi Iheanacho, Najeriya bayan sun doke Masar
please wait

No media source currently available

0:00 0:01:11 0:00
Karin bayani akan Wasanni
XS
SM
MD
LG