Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Ukraine Zata Mayarwa Rasha Martani - inji Hukumomi


Sojojin Rasha a cikin tsohon sansanin sojin Ukraine dake Kirimiya.
Sojojin Rasha a cikin tsohon sansanin sojin Ukraine dake Kirimiya.

Hukumomin Ukraine sun jaddada cewar rundunar sojin kasar a shirye take ta maida martani ga duk wani yunkurin mamayen daka iya zuwa daga sojin kasar Rasha da yanzu ke dannowa zuwa kan iyakokin Ukraine.

Mukaddashin shugaban Ukraine Oleksandr Turchynov ya bayyanawa zaman taron majalisar Ministoci a birnin Kyiv yau laraba, cewar lallai kam akwai babbar barazanar cewa Rasha ka iya shirya yaki a tsakanin masu rigima da juna a Ukraine domin ta sami sukunin tsoma baki.

A dai dai lokacin da ake wannan cece-ku cen ne kuma mayakan dake samun goyon bayan Rasha ke samun nasarar kwace wani muhimmin ginin ofishin gudanar da mulki a gabashin Ukraine.

Rahotannin na cewa daruruwan mayakan dake samun goyon bayan Rasha dauke da makamai ne suka je suka mamaye gine-ginen Gwamnati a kusa da kan iyaka da kasar Rasha.
XS
SM
MD
LG