Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Umar Abdulmuttalab da Aka Yiwa Daurin Rai da Rai a Amurka Ya Shigar da Kara Kotu


Zanen Umar Faruk Abdulmuttalab da lauyan dake taimakonsa, cikin wata kotun birnin Detroit.

Umar Abdulmuttalab wani dan Najeriya da ya yi yunkurin tarwatsar da wani jirgin sama dauke da fasinjoji 300 a shekarar 2009 ya shigar da kara kotu kan halin da yake ciki a gidan kaso inda yake daurin rai da rai

Dan Najeriyan nan da ya boye bam a cikinwandansa har yayi kokarin tawrwatsa wani jirgin saman pasinja na Amurka a shekarar 2009, ya shigar da ‘kara kan cewa an take masa hakkinsa da tsarin mulki ya bashi a gidan yari.

A cikin karar da ya shigar makon da ya gabata a wata kotun tarayya dake jihar Colorado ta nan Amurka, Umar Faruk Abdulmutallib, yayi korafin cewa an kebance shi guri guda a gidan yarin, an kuma hana shi ganawa ko magana da danginsa, sannankuma an hana shi yin ibadar addininsa na musulunci.

Haka kuma Umar Abdulmuttalab ya yi zargin cewa an tilasta shi cin abincin da ba halal ba, kuma lokaci da yayi yunkurin yin yajin cin abinci don nuna rashin jin dadin abubuwan da ake yi masa, an yi mishi ‘durar abinci ba tare da amincewarsa ba.

Shi dai Abdulmutallib, yana gidan wakafi ne a jihar Colorado, wanda shine gidan yari mafi tsaro a Amurka, bayan da aka yanke masa hukuncin ‘daurin rai da rai na tsawon rayuwadaya bayan daya har sau hudu.

Abdulmutallib dai yayi kokarin tayar da bam ne a cikin wani jirgin saman da ke ‘dauke da mutane fiye da 300, amma hakarsa bata cimma ruwa ba, bayan da sauran fasinjojin da ma’aikatan jirgin suka abka mishi, suka cafke shi har zuwa lokacinda jirgin ya sauka a filin saukar jirage na birnin Detroit.

Facebook Forum

Shin PI Za Ta Fashe Kuwa Ko Yaudara Ce Kawai?

Karin bayani akan Bidiyo
XS
SM
MD
LG