Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Ummi Zeezee Ta Gana Da Kwamishinar Mata Ta Kano Kan Yunkurin Kashe Kanta


Kwamishinar Mata, Zahra'u Muhammad, hagu Ummi Zeezee, dama (Instagram / Ummizeezee).
please wait

No media source currently available

0:00 0:00:22 0:00

Kwamishinar Mata, Zahra'u Muhammad, hagu Ummi Zeezee, dama (Instagram / Ummizeezee).

Ummi ta kuma nuna takaicinta kan yadda mutane da dama suka yi ta "zaginta" a lokacin da al’amarin ya faru, tana mai cewa kamata ya yi, a yi mata nasiha ba a ci mata mutunci ba.

Fitacciyar jarumar masana’antar Kannywood a Najeriya Ummi Ibrahim, wacce aka fi sani da Ummi Zeezee, ta gana da Kwamishinar mata ta Kano Zahra’u Muhammad bayan da jami’ar gwamnatin ta nemi ta ganta kamar yadda Ummi ta fada.

Ganawar ta su na zuwa ne, bayan da a farkon watan Afrilu, Ummi ta wallafa a shafinta na Instagram cewa, tana ji kamar ta kashe kanta.

Ba a san takamaiman lokacin da suka gana ba, amma a karshen makon da ya gabata Ummin ta wallafa hotunta tare da kwamishinar.

Ummi Ibrahim Zeezee (Instagram/ Ummi Zeezee)
Ummi Ibrahim Zeezee (Instagram/ Ummi Zeezee)

“Malama Zahra’u na je mun zauna ta min nasiha ne sosai mai ratsa jiki, da na ce zan kashe kaina.” Ummi ta rubuta a shafinta na Instagram.

“Don haka, ina godiya ta musamman zuwa ga kwamishina Zahra’u, dangane da yadda ta nuna damuwarta har ta ce in zo ta ji matsalar da ta sa nake so na kashe kaina."

Karin bayani akan: Ummi Zeezee, Kannywood, Kano, Nigeria, da Najeriya.

Ummi ta kuma nuna takaicinta kan yadda mutane da dama suka yi ta "zaginta" a lokacin da al’amarin ya faru, tana mai cewa kamata ya yi, a yi mata nasiha ba ci mata mutunci ba.

Ta kara da cewa, "ban san lokacin da na fashe da kuka ba, domin ni na dade ban ga mace mai imani da sanin darajar rayuwar dan adam ba."

Jarumar dai ta yi ikrarin cewa wani abokin harkarta ne dan kabilar Igbo ya damfare ta naira miliyan 450 a wata harkar mai da suka kulla.

Hakan ta ce ya sa, ta fara tunanin kashe kanta, saboda kuncin rayuwa da ta shiga sanadiyyar wannan damfara.

Wannan batu ya janyo ce-ce-ku-ce a Kannywood da kuma daga masu bibiyar fina-finan masana’antar wacce ke arewacin Najeriya.

Bayan kwanciyar kurar wannan lamari, Ummi ta wallafa a shafinta na Instagram cewa, ta ji labarin kwamishinar na so ta ganta, abin da ya kai ga wannan haduwa.

Jaruma Ummi, ta yi fitattun fina-finai irinsu ”Jinsi,” “Gambiza” da "Tutar So" ta kuma yi fina-finai da manyan jarumai irin su Ali Nuhu, marigayi Ahmed S. Nuhu, Abba El Mustapha da Ibrahim Mai Shunku.

Saurari Dalilin Da Ya Sa Ummi Zeezee Ta Ce Tana So Ta Kashe Kanta A Hira Da Wakiliyar VOA Baraka Bashir
please wait

No media source currently available

0:00 0:06:39 0:00

Bidiyo

Saurari Dalilin Da Ya Sa Ummi Zeezee Ta Ce Tana So Ta Kashe Kanta A Hira Da Wakiliyar VOA Baraka Bashir
please wait

No media source currently available

0:00 0:06:39 0:00
Karin bayani akan Bidiyo

VOA CASU

VOA CASU: Saurari Bayanin Jarumar Kannywood, Nafeesa Abdullahi
please wait

No media source currently available

0:00 0:12:24 0:00
Karin bayani akan Bidiyo

VOA CASU

VOA CASU: Bikin Yini Na Auren Zawarawa A Kano
please wait

No media source currently available

0:00 0:02:27 0:00
Karin bayani akan Bidiyo
XS
SM
MD
LG