Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Za Mu Saki Fim Din “Labarina 3” Bayan Azumi – Aminu Saira


Fim Labarina (Instagram/nuhuabdullahi)
Fim Labarina (Instagram/nuhuabdullahi)

Sai dai sanarwar da darekta Aminu Saira ya fitar, ba ta ambaci kafa ko tashar da za a haska fim din na Labarina ba.

Za a saki fim din “Labarina” kashi na 3 mai dogon zango da kamfanin Saira Movies ke shiryawa bayan watan azumi, in ji Darektan fim din Aminu Saira.

Saira ya bayyana hakan ne a shafinsa na Instagram a ranar Lahadi.

“Insha Allah #Labarina S3 zai fara zuwa muku bayan Ramadan.” Saira ya rubuta a shafinsa - aminusaira.

“Allah ka sa mu fita kunyar masu kallo,” ya kara da cewa.

Aminu Saira (hagu) Nuhu Abdullahi (Mahmud - dama)
Aminu Saira (hagu) Nuhu Abdullahi (Mahmud - dama)

Labarina wanda aka kammala nuna zango na 2 a farkon watan Janairu, gawurtaccen fim ne da ya samu karbuwa a tsakanin masoya fina-finan Hausa a ciki da wajen kasar Hausa.

Fim din, wanda Nazir Sarkin Waka da Nazifi Asnanic suka shirya, na kunshe da ala’amrun da suka shafi soyayya, karatun jami’a, yaudara, son duniya, rikon amana da dai sauransu.

Ya kuma hada fitattun jaruman masa’antar Kannywood irinsu Nafisa Abdullahi (Sumayya) Nuhu Abdullahi (Mahmud) Isa Feroz Khan (Presdo) Teema Yola, Ibrahim Bala, Hafsa Idris da Hadiza Saima.

Tuni dai masu bibiyar shirin suka fara tsokaci kan wannan sanarwa da aka fitar – mafi aksarinsu suna masu tambaya kan kafar da za a haska fim din.

Lokacin da ake daukan Labarina Kashi na 3 (Instagram/aminusaira)
Lokacin da ake daukan Labarina Kashi na 3 (Instagram/aminusaira)

“Muna godiya bisa jajircewarku wajen ganin kun faranta mana rai, sannan kuma a wacce tasha za ku fara haska mana? Haleelumusaa ya tambaya a shafin Instagram.

A baya, an yi ta yamadidin cewa an samu rashin jituwa tsakanin kamfanin na Saira Movies da ke da hakkin mallakar fim din, da tashar Arewa 24 da ta haska zango na da na biyu.

Amma Saira ya fito ya musanta hakan, yana mai cewa labarin kanzon kurege ne.

Sai dai a wannan sanarwa da ya fitar ta fara nuna kashi na 3 na fim din, Saira wanda shi ya shirya fitaccen fim din "Dan Marayan Zaki" bai ambaci kafa ko tashar da za a haska fim din na Labarina ba."

Bidiyo

Saurari Dalilin Da Ya Sa Ummi Zeezee Ta Ce Tana So Ta Kashe Kanta A Hira Da Wakiliyar VOA Baraka Bashir
please wait

No media source currently available

0:00 0:06:39 0:00
Karin bayani akan Bidiyo

VOA CASU

VOA CASU: Saurari Bayanin Jarumar Kannywood, Nafeesa Abdullahi
please wait

No media source currently available

0:00 0:12:24 0:00
Karin bayani akan Bidiyo

VOA CASU

VOA CASU: Bikin Yini Na Auren Zawarawa A Kano
please wait

No media source currently available

0:00 0:02:27 0:00
Karin bayani akan Bidiyo
XS
SM
MD
LG