Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Majalisar Dinkin Duniya na Son a Gaggauta Hukunta Wadanda su ka Aikata Fyade a Kongo


Wata babbar jami’ar Majalisar Dinkin Duniya ta ce dole ne a gurfanar da shugabannin yan tawayen Kongo, kan zargin fayde tun kafin batun ya shiririce.

Wata babbar jami’ar Majalisar Dinkin Duniya da ke cikin wadanda aka nada don su hana fyade a yankunan da ake yaki, ta ce dole ne a gurfanar da shugabannin yan tawayen Congo, da ake zargi da daure ginda wa masu fayde wa tarin mata tun kafin batun ya shiririce.

Wakiliyar Majalisar Dinkin Duniya na musamman Margot Wallstrom ta fadi a wurin taro a Geneva jiya Litini cewa, dokar kasa da kasa bata bayar da cikakkiyar kariya ga mata daga fyade saboda ba a cika aiki da ita ba.

Ta ce ana bukatar daukar matakan gaggawa don hukunta wadan da suka sa sojojin yan tawaye su ka yi wa a kalla mata 300 fyade a Janhuriyar Demokaradiyyar Congo a watannin Yuni da Agusta

XS
SM
MD
LG