Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Shugaban Amurka Barack Obama yace Amincewa 'Yarjejeniyar Rage Makaman Nukiliya Da Rasha Yana Da Muhimmancin Ga Tsaron Amurka.


Shugaba Barack Obama yake magana a fadar White a wani taro gameda shirin rage makaman Nukiliya da Rasha.

Alhamis ne shugaban ya yi wan nan kira bayan ya gana da tsoffin manyan jami'an difilomasiyya da suka yi aiki da gwamnatocin baya.

Shugaban Amurka Barack Obama yace yana da muhimancin gaske ga tsaron Amurka ganin an amince da yarjejeniyar rage yawan makaman Nukiliya da kasar Rasha.

Yau Alahamis ce shugaban ya yi wan kira bayan ya gana da tsoffin manyan jami’an difilomasiyya da suka aiki da tsoffin gwamnatocin Amurka.

Yarjejeniyar ta ayyana rage yawan makaman Nukiliya d a aka girka da kamar kashi 30,amma ana samun jinkirin amincewa da ita sakamakon damuwa da wasu wakilan daga jam’iyyar Republican suka nuna.

XS
SM
MD
LG