Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Usman Dan Fodio Shi ya Fara Hada Sassan Najeriya


Sarkin Musulmi Sa'ad Abubaka III

An yi taron tunawa da Shehu Usmanu Dan Fodio na shekara shekara da Muslmai ke shiryawa a Abuja

Kowace shekara Musulmai na yin taron tunawa da Shehu Usmanu Dan Fodio. An yi na wannan shekarar a Abuja inda aka tuna da irin tsarin mulki da ya kafa da koyaswa da ya yi.

Inda shugabannin Najeriya zasu yi koyi da irin shugabancin Shehu Usmanu Dan Fodio da ko kasar ta samu cigaba. Ya kafa mulki mai adalci. Ya nuna halin saukin kai da dogaro da kuma yada addinin Musulunci.

A taron na bana Farfasa Dahiru Yahaya na Jami'ar Bayero dake Kano shi ne babban mai jawabi. Ya ce Shehu Usmanu Dan Fodio shi ya fara hada sansanoni daban daban na Najeriya ya mayar da su daula daya kimanin shekaru dari biyu da suka wuce. Ya hada Hausa bakwai da banza bakwai. Shi ya kafa dauloli a Gombe, Filato, Bauchi da Kwara da kasashen Hausa aka samu babbar daula wanda babu irinta duk fadin Afirka.

Shugaban wadanda suka dauki nauyin shirya taron Mohammed Awal ya ce gwagwarmayar Shehu Usmanu Dan Fodio ta sa suka zama mutane yau.Idan ba dominsa ba da kila mafi yawansu zasu zama maguzawa. Makasudin taron shi ne a tunashe da jama'a irin rayuwar da Shehu Usman ya yi domin a koyi daratsi dasu a gyara rayuwa.

Idan an ce mutum bamaguje ne to wanda ba Musulmi ba kenan. Kowa ya san ma'anar maguzanci. Yadda sarakunan maguzawa ke gudanar da mulkinsu kamar su Dan Gwarzo, da Shuhu Usman bai yakesu ba ya maye gurbinsu da mulki mai adalci ya kuma kawo Musulunci to da an cigaba da mulkin danniya. A wancan lokacin idan sarki ya zo rangadi to duk wanda ya yi sabon aure dole ya fita daga gidansa ya bar matarsa ma daya daga cikin 'ya'yan sarki. Dole kuma a yanka ma sarki kaji kana a yi tsafi da bori.

Shehu Usmanu Dan Fodiowanda ya kafa cibiyarsa a Sokoto ya rasu a shekarar 1817 bayan ya kafa mulki bisa ga addinin Musulunci ya kuma kawar da shaidanci da bidi'o'i.

Ga rahoton Nasiru Adamu El-Hikaya.

please wait

No media source currently available

0:00 0:02:59 0:00
Shiga Kai Tsaye

Shin PI Za Ta Fashe Kuwa Ko Yaudara Ce Kawai?

Karin bayani akan Bidiyo
XS
SM
MD
LG